Bambamci tsakanin maniyyi da maziyyi dakuma wanda yake karya azumi.

1.      Maniyyi.

Maniyyi shine me kauri wanda shi baya fita saida matukar sha,awa kuma zaka ganshi fare ne kuma yanada kauri sannan kuma yanan fita ne da karfi kuma yana fita dayawa.

Yayinda mutum yasadu da iyalinsa kokuma mutum yayi istimna,i ta hanyar dazaisashi yafita kuma yana fita dakargfine sosai kumkan zaka ganshi farene mekauri.

2.      Waziyyi.

Shikuma waziyyin siririne shima daiv farine amma bashida kaurin maniyyi kuma shi baya fita dayawa hasalima shi zakaga diga yakeyi.

Kumashi yana fitane alokacin karamar sha,awa kamar irin tinanin abun tsaraici ko kuma jin muryar mace dadai sauransu.

                             shin wannene yake karya azumi?

Maniyyi:

Shi maniyyi shine fitar dashi tahanyar istimna,i ma,ana ya kakalosa kodaba tahanyar jima,i ba to a mazhabar malikiyya azuminsa yakarye kuma saiyayi kaffara.

Idan yafitar dashi koda shafa al,aurarsa koda shafar mace koyayta kallonta kallo wanda zaitayar da sha,awa ko kallon fina-finan batsa ko amfani da subulu dadai sauransu to azuminsa yakarye kuma saiyayi kaffara.

Amma idan da tunanine haryakwo maniyyi to ramuwa zaiyi babu kaffara.

Amma ida yana sane yaita kallon mace kallon dazai tayar da sha,awa ko yaita sauraran kalamanta harya tayar dasha,awar sa to wannan akwai ramuwa da kuma kaffara.

Misali:-

Zakaga samari da yawa suna waya da yammata da rana awatan ramadan kuma zakaga yawanci muryar yan,matan tana tayar musu da sha,awa amma bazasu hakura sai da daddara ba bayan ansha ruwa, har sai sunkawo maniyyi saboda dadin muryarta to azumin ka yakarye kuman saikayi kaffara .

Wannan amazhabar malikiyya kenan, amma asauran mazhabobin shafi,iyya da hunabila sunce ramuwa kawai zaiyi babu kaffara.

Waziyyi:-

Shiko maziyyi idan yafitar da waziyyi ne tahanyar kallo ko zance ko taba ,mace to azumin yakarye zaiyi ramuwa amma babu kaffara.

Amma idan yakawo waziyyin ne tahanyar tunani kon mafarki to azuminsa yananan.

Wannan shine bambamci tsakanin maniyyi da waziyyi da kum,a wanda yake karya azumi muna fatan kungane.

Muna goodiya da ziyartar shafinmu.